MATIYU 1

1Littafin tarihin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda wanda shi ma ɗan Ibrahim ne. 2Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakub, Yakub ya haifi Yahuda da ˈyanˈuwansa. 3Yahuda ya haifi Ferez da Zera. Mamarsu kuwa Tamar. Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Aram, 4Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon. 5Salmon ya haifi Bowaz. Mamarsa kuwa Rahab ce. Bowaz ya haifi Obed. Mamarsa kuwa Rut ce. Obed ya haifi Yesse, 6Yesse ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon. Mamarsa kuwa Batsheba wadda dā matar Uriya ce. 7Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, 8Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Uzziya, 9Uzziya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya, 10Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya, 11Yosiya ya haifi Yekoniya da ˈyanˈuwansa, a lokacin da aka kwashi mutanen Yahuda zuwa bauta a ƙasar Babila. 12Bayan da aka kai su Babila, Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel, 13Zerubbabel ya haifi Abihud, Abihud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor, 14Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim ya haifi Eliyud, 15Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yakub, 16Yakub ya haifi Yusuf mijin Maryamu, Maryamu ta haifi Yesu wanda ake ce da shi Almasihu. 17Wato dukan tsara daga Ibrahim zuwa Dawuda, tsara goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa lokacin da aka kwashi Israˈilawa zuwa bauta a Babila, tsara goma sha huɗu ce, daga bauta a Babila kuma zuwa haifuwar Almasihu, tsara goma sha huɗu ce. 18Ga yadda aka haifi Yesu Almasihu. Lokacin da Yusuf yake neman Maryamu mamar Yesu da aure, tun ba a ɗaura musu aure ba, sai ya zama tana da ciki daga Ruhu Mai Tsarki. 19Saurayinta Yusuf yana da kirki, kuma ba ya so yă ba ta kunya a cikin mutane, sai ya yi tunani yă sake ta shiru a ɓoye. 20Amma yana cikin wannan tunani sai ga wani malaˈikan Ubangiji ya bayyana gare shi a mafarki, ya ce masa, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu ta zama matarka domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za ta haifi ɗa, za ka sa masa suna Yesu domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22Dukan wannan ya faru ne domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi cewa, 23“Budurwa za ta yi ciki, ta haifi ɗa za a kuma sa masa suna Immanuwel.” Maˈanar Immanuwel ita ce, “Allah yana tare da mu.” 24Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin malaˈikan Ubangiji. Yusuf kuwa ya ɗauki Maryamu ta zama matarsa. 25Amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.


Copyrighted Material
Learn More

will be added

X\